IQNA

Zaman Taro Kan Saka Hannayen Jari A Bangaren Yawon Shakata A Demascus

Bangaren al’adu da fasaha, za a gudanar da wani taron kara juna sani a karon farkon kan saka hannayen jari a bangaren yawon shakatawa a kasashen musulmi, wanda ake sa ran zai gudana a birnin Demascus fadar mulkin kasar Syria tare da halartar masana da kuma ‘yan kasuwa masu saka hannayen jari na kasashen ketare.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, za a gudanar da wani taron kara juna sani a karon farkon kan saka hannayen jari a bangaren yawon shakatawa a kasashen musulmi, wanda ake sa ran zai gudana a birnin Demascus fadar mulkin kasar Syria tare da halartar masana da kuma ‘yan kasuwa masu saka hannayen jari na kasashen ketare musamman daga kasashen larabawa da na musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai yi dubi kan hanyoyin da ya kamata a bi domin saka hannayen jari wanda hakan zai iya habbaka dukkanin bangarori na yawon shakatawa da bude a cikin kasashen musulmi, musamman idan aka yi la’akari da irin muhimmancin da wannan bangare yake da shi a cikin kasashen musulmi.
Za a gudanar da wani taron kara juna sani a karon farkon kan saka hannayen jari a bangaren yawon shakatawa a kasashen musulmi, wanda ake sa ran zai gudana a birnin Demascus fadar mulkin kasar Syria tare da halartar masana da kuma ‘yan kasuwa masu saka hannayen jari na kasashen ketare.
774483