IQNA

Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron gidan sarautar Ali khalifa a kasar Bahrain da kuma na kasar saudiyya sun kai farmaki kan masallacin Imam Ali (AS) da ke kasar Bahrain, da nufin murkushe hankoron al'ummar kasar na neman a gudanar canji cikin harkokin siyasa da mulkin kasar, wanda gidan sarauta iko da shi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar al'alam cewa, jami'an tsaron gidan sarautar Ali khalifa a kasar Bahrain da kuma na kasar saudiyya sun kai farmaki kan masallacin Imam Ali (AS) da ke kasar Bahrain, da nufin murkushe hankoron al'ummar kasar na neman a gudanar canji cikin harkokin siyasa da mulkin kasar, wanda gidan sarauta iko da shi tsawon shekaru.

Bayanin ya ci gaba da cewa akwai wasu daga cikin masu kokarin nuna abin da ke faruwa a kasar Bahrain a matasayin wani lamari na mazhaba ko bangaranci tsakanin al'umma da kuam mahkunta, wanda hakan ya yi hannun riga da abin da ya ke gaskiya a kasar ta Bahrain, inda mutane suke bukatar da a gudanar da sauye-sauye a cikin harkokin siyasar kasar, maimakon tafiya kan tafarkin yanzu.

Manyan malaman addinin muslunci a kasar Lebanon sun yi kakkausar suka da kuma yin Allawadai da cin zarafin da mahukuntan kasashen Bahrain da Saudiyya suke yi kan al'ummar Bahrain, ta hanyar murkushe zanga-zangarsu ta lumana da karfin tuwo, da kuma afkawa kan masallatansu da wuraren ibadarsu da nufin wanzuwar sarautar kasashen biyu.

Jami'an tsaron gidan sarautar Ali khalifa a kasar Bahrain da kuma na kasar saudiyya sun kai farmaki kan masallacin Imam Ali (AS) da ke kasar Bahrain, da nufin murkushe hankoron al'ummar kasar na neman a gudanar canji cikin harkokin siyasa da mulkin kasar, wanda gidan sarauta iko da shi.
776196
An Karbe Dubban Kur'anai Da Aka Buga Da Kuskure