IQNA

13:07 - April 21, 2011
Lambar Labari: 2109539
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan gidan sarautar Saudiyya da ke bin tafarkin akidar wahabiyanci sun kame wani marubuci mabiyin tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalanm gidansa Nazir Majid, mazaunin birnin Alkhabar da ke yankin gabacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na 20minutes an bayyana cewa, mahukuntan gidan sarautar Saudiyya da ke bin tafarkin akidar wahabiyanci sun kame wani marubuci mabiyin tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalanm gidansa Nazir Majid, mazaunin birnin Alkhabar da ke yankin gabacin kasar ta Saudiyya.
A wani baynain kuma babban malamin addini na kasar Bahrain Abdulkarin Abduljalil ya bayyana cewa, mutanen kasar Bahrain sun mabiya mazhabar shi’a da ‘yan sunna na kasar sun rayu tsawon shekaru a kasar ba tare da wata matsala ba, amma a lokacin da suka fara bore domin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar sai gidana sarauta mayar da maganar ta mazhabanci domin samun damar murkushe masu bore a fadin kasar.
Malamin ya ci gaba da cewa babu wani dalili da zai sanya mahukuntan Bahrain su fake da batun mazhaba domin murkushe masu gudanar da zanga-zangar neman sauyi na siyasa akasar, tare da tabbatar da tsarin kama karya kansu, domin kuwa kowa aduniya ya san abin da ke faruwa ba shi da wata dangantaka da batun mazhaba kamar yadda gidanasarautar da masu kare daga kasashen larabawa suke rayawa.
Al’ummar kasar Bahrain sun mabiya mazhabar shi’a da ‘yan sunna na kasar sun rayu tsawon shekaru a kasar ba tare da wata matsala ba, amma a lokacin da suka fara bore domin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar sai gidana sarauta mayar da maganar ta mazhabanci domin samun damar murkushe masu zanga-zangar lumana.
777718


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: