IQNA

Ana Shirin Gina Wani Wurin Ajiyen Kayan Tarihin Muslunci A Kasar Australia

16:31 - May 04, 2011
Lambar Labari: 2117513
Bangaren kasa da kasa, an shirin gina wani wurin ajiye kayan tarihin muslunci a kasar Australia, da nufin kawar da mummunar fahimtar da aka saka cikin kwakwalen al’ummar kasar dangane da addinin musulunci da koyarwarsa, wanda kuma hakan na daga cikin abin da ake yi a mafi yawan kasashen turai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an shirin gina wani wurin ajiye kayan tarihin muslunci a kasar Australia, da nufin kawar da mummunar fahimtar da aka saka cikin kwakwalen al’ummar kasar dangane da addinin musulunci da koyarwarsa, wanda kuma hakan na daga cikin abin da ake yi a mafi yawan kasashen turai domin bayar da wata sura mai muni kan addinin muslunci a cikin zukatan mutane.
Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin abubuwan da za a yi har da kafa wani wurin baje koli na kayan al’adun musulunci a birnin Molbon, inda za akawo kayan tarihi da kuma bubuwan fasaha a na addinin muslunci wadanda wasu suke komawa zuwa ga kasar ta Austaralia, domin tabbatar wa mutanen kasar cewa addinin muslunci ba bako ba ne a kasar.
Gina wurin ajiye kayan tarihin muslunci a kasar Australia, da nufin kawar da mummunar fahimtar da aka saka cikin kwakwalen al’ummar kasar dangane da addinin musulunci da koyarwarsa, wanda kuma hakan na daga cikin abin da ake yi a mafi yawan kasashen turai, hakan na da matukar muhimmanci wajen wayar da kan al’ummar kasar. 785563
captcha