Bangaren siyasa da zamantakewa: Tanzaniya ta sanar da cewa bada bashi domin sayan gida karkashin Stanbic za a bayar da shi ne karkashin dokokin da tsarin addinin musulunci ga yan kasar
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Tanzaniya ta sanar da cewa bada bashi domin sayan gida karkashin Stanbic za a bayar da shi ne karkashin dokokin da tsarin addinin musulunci ga yan kasar. Wannan tsari na bayar da bashi domin sayan gida da muhalli wani tsari ne mai karfi da kuma mai inganci da zai taimakawa yan kasar ta Tanzaniya karkashin tsari irin na musulunci da dokokinsa musamman idan aka yi la'akari da yadda bayar da bashi a karkashin tsarin yan jari hujja na ruguza zamantakewa da karfiun shigar mutane masu tasowa ta fuskar tattalin arziki.
796354