IQNA

An Wake Ministan faransa daga Zargin Cin Fuska Ga Musulmi

15:54 - June 12, 2011
Lambar Labari: 2136911
Bangaren kasa da kasa: A jiya ne ashirin ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kotun kasar Faransa CJR ta wanke ministan kasar Faransa Klod Ganan daga zargin cin fuska ga musulmi da kuma yin bayanai da suka shafi banbanci da wariya wannan hukumci ya zone a daidai lokacin da majalisar dinkin duniya ta soki yadda ake nuna siyasar wariya da siyasar danne kananan kabili da wariya a kasar ta faransa.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; A jiya ne ashirin ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kotun kasar Faransa CJR ta wanke ministan kasar Faransa Klod Ganan daga zargin cin fuska ga musulmi da kuma yin bayanai da suka shafi banbanci da wariya wannan hukumci ya zone a daidai lokacin da majalisar dinkin duniya ta soki yadda ake nuna siyasar wariya da siyasar danne kananan kabili da wariya a kasar ta faransa.A yan shekarun nan na baya-baya ana fuskantar siyasar wariya da banbanci da kuma bayanai da maganganun nuna wariya da banbancin launin fata ada kuma musamman wariyar addini a siyasar day akin neman zabe da mukami a kasar ta faransa lamarin da ked a ban tsoro da fargaba kan makomar zamnatewar al'ummar kasar da kuma dangantakarsu da sauran al'ummomi da ke zaune a cikin kasar da kuma wadanda ke ketare da kuma irin wannan siyasa na iya watsuwa zuwa ketare da sauran kasashen yammacin turai da yin kamari.


806169
captcha