IQNA

A Daren Yau Ne Za A Fara Gasar Karatun Kur'ani Ta Kasa a Malazia

14:06 - June 14, 2011
Lambar Labari: 2138171
Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani ta kasa baki daya a daren yau a birnin Kualalapour fadar mulkin kasar Malazia, tare da halartar daliban makarantun kur'ani mai tsarki daga sassan kasar, da kuma fitattun alkalan gasar kur'ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani ta kasa baki daya a daren yau a birnin Kualalapour fadar mulkin kasar Malazia, tare da halartar daliban makarantun kur'ani mai tsarki daga sassan kasar, da kuma fitattun alkalan gasar kur'ani mai tsarki da suka yi fice.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa ana gudanar da ita a kowace shekara a kasar ta Malazia, inda wannan karon za a gudanar da ita a karo na hamsin da hudu, duk kuwa da cewa daliban da za su shiga cikin gasar da dama daga cikinsu wannan shi ne karo na farko da za a fara ganinsu a wanna fage.
za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani ta kasa baki daya a daren yau a birnin Kualalapour fadar mulkin kasar Malazia, tare da halartar daliban makarantun kur'ani mai tsarki daga sassan kasar, da kuma fitattun alkalan gasar kur'ani mai tsarki.
807736


captcha