IQNA

14:04 - June 14, 2011
Lambar Labari: 2138173
Bangaren kasa da kasa, Limaman masallatan kasar Mauritania sun fara samun horo a wani shiri na koyar da su muhimman abubuwan da ya kamata su sani na limancin masallatai a fadin kasar, bisa la'akari da yawan musulmin kasar da kuma masallatai.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqn aya habrta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, limaman masallatan kasar Mauritania sun fara samun horo a wani shiri na koyar da su muhimman abubuwan da ya kamata su sani na limancin masallatai a fadin kasar, bisa la'akari da yawan musulmin kasar da kuma masallatai, gami da yawan masallata da suke bukatar hananuka mai sanda daga limaman masallatai.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shirin na daga cikin muhimman ayyukan da ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta saba gudanarwa a kowace shekara, musamman ma ganin cewa lokacin gudanar da ayyukan ibada na musamman wato watan Ramadan mai alfarma yana ta karatowa.
Limaman masallatan kasar Mauritania sun fara samun horo a wani shiri na koyar da su muhimman abubuwan da ya kamata su sani na limancin masallatai a fadin kasar, bisa la'akari da yawan musulmin kasar da kuma masallatai an kasar.
807765


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: