Bangaren kasa da kasa: gidan talbijin na tauraron dan adam na Hafiz da ke watsa shirye-shiryensa daga kasar Masar a karon farko daga watan Sha'aban da yayi daidai da watan Tir zai watsa shiri kai tsaye day a kumshi shirin bayyana abubuwan al'ajabi na ilimi a cikin Alkur'ani mai girma da kuma sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa; gidan talbijin na tauraron dan adam na Hafiz da ke watsa shirye-shiryensa daga kasar Masar a karon farko daga watan Sha'aban da yayi daidai da watan Tir zai watsa shiri kai tsaye day a kumshi shirin bayyana abubuwan al'ajabi na ilimi a cikin Alkur'ani mai girma da kuma sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa.Malamai da kuma masana kur'ani mai girma da kuma hadisan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a agare shi da kuma alayan gidansa za su rika yin bayani da sharhi kan fannonin ilimi na banmamaki da ke cikin littafin Allah mai girma da kuma hadisai.
808527