Bangaren fasaha; zane zane a al'adun da fasahar musulunci nada matsayi mai girma fiye da zahirinsa mai kyau da kayatarwa domin yana isar da sako na badini .
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; zane zane a al'adun da fasahar musulunci nada matsayi mai girma fiye da zahirinsa mai kyau da kayatarwa domin yana isar da sako na badini .Zane zane nada matsayi da gurbi a cikin rayuwa da zamantakewar dan adam tun asali domin ta wannan hanya ce dan adam na farko ya bi yake bayyana wani abu ko wani ilimi da fadakarwa ga sauran mutane da yake rayuwa da su ko al'ummar da za ta zo a nan gaba domin sanin yadda ya rayuwa da ci gaban day a samu ko kumja yadda za fahimci wani abu da yake son bayyanawa kuma addani ma na tunkahu da wannan bangare na ilimi da salo da kuma ya kumshi kyau na zahiri.
810399