Bangaren kasa da kasa; a ranar sha biyu ga watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ya zuwa ranar biyar ga watan Shahrivar shikara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiyar za a farad a kamala zagon karatun kur'ani mai girma na musamman na lokacin bazaar a kasar Faransa ga yara kanana da kuma wadanda wannan shi ne karon farko da za su karanta kur'ani mai girma kuma a garin Chateau Chinon ne za a gudanar da wannan zangon karatu.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a ranar sha biyu ga watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ya zuwa ranar biyar ga watan Shahrivar shikara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiyar za a farad a kamala zagon karatun kur'ani mai girma na musamman na lokacin bazaar a kasar Faransa ga yara kanana da kuma wadanda wannan shi ne karon farko da za su karanta kur'ani mai girma kuma a garin Chateau Chinon ne za a gudanar da wannan zangon karatu. Kuma duk wani mai bukatar shiga wannan zangon karatu da kuma samin karuwa da sani ta fuskar ilimin kur'ani da kira'a yana iya ziyartar shafin internet na www.iesh.org/index.php?lang=fr da kuma rubuta sunansa.
810913