Bangaren al'adu da fasaha, a lokacin da shugaban jami'ar nazari kan addinai da mazhabobin muslunci da kasa da kasa da ke birnin Tehran ya tafi zuwa kasar Bosnia, ya gana da wasu daga cikin shugabannin cibiyoyin addini a birnin Sarayevo fadar mulkin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hula da jama'a na maja'ama'ar Ahlul bait an bayyana cewa, a lokacin da shugaban jami'ar nazari kan addinai da mazhabobin muslunci da kasa da kasa da ke birnin Tehran ya tafi zuwa kasar Bosnia, ya gana da wasu daga cikin shugabannin cibiyoyin addini a birnin Sarayevo fadar mulkin kasar, inda suka tattauna muhimamn batutuwa da suka danganci harkokin addini da yadda za a kara bunkasa sa su.
Babbar cibiyar hada-hadar kasuwanci ta birnin Tehran an bayyana cewa, kwamitin hadin gwiwa tsakanin jamhuriyar muslunci ta Iran da kuma kasar Bosnia kan harkokin kasuwanci ya fara aiki a hukumance daga wannan mako da muke ciki, bayan kaddamar da shi tare da halartar jami'ai daga dukaknin kasashen biyu na Bosnia da kuma Iran.
A lokacin da shugaban jami'ar nazari kan addinai da mazhabobin muslunci da kasa da kasa da ke birnin Tehran ya tafi zuwa kasar Bosnia, ya gana da wasu daga cikin shugabannin cibiyoyin addini a birnin Sarayevo fadar mulkin kasar ta Bosnia, inda nan akasarin cibiyoyin addini suke da mazauni.
830303