IQNA

An Gano Maboyar Shugaban Mulkin Kama Karya Na Libya

11:46 - September 05, 2011
Lambar Labari: 2181586
Bangaren kasa da kasa, Abdulhakim Bilhaj shugaban kwamitin soji da ke mulkin birnin Tripoli ya fadi a daren jiya sun gano inda Gaddafi yake boye amma dai za su ci gaba da boye lamarin har sai sun kama ga hannu.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar al-alam an bayyana cewa, Abdulhakim Bilhaj shugaban kwamitin soji da ke mulkin birnin Tripoli ya fadi a daren jiya sun gano inda Gaddafi yake boye amma dai za su ci gaba da boye lamarin a halin yanzu, sai a nan gaba idan sun cafke shi za su sanarwa duniya halin da ake ciki.

Wani labarin kuma yana cewa gwamnatin rikon kwaryar Libya ta bada wa'adin zuwa gobe lahadi da safe ga mutanen garin Bani- Walid da su mika kai ko kuma fuskanci yaki jami'in sojan da ke karkashin gwamnatin rikon kwaryar a garin Tarhuna, Abdur-Razaq Nadhuly ya fada a yau asabar cewa: masu bore sun gargadi shugabannin kabila na Bani Walid da su daga farar tuta ko kuma su fuskanci yaki daga nan zuwa sa'oi ashirin da hudu.

Daya daga cikin 'ya'yan hambararren shugaban kasar Libya Mu'ammar Khaddafi, Sa'idy yana da mafaka acikin garin na Bani Walid, a gefe daya gwamnatin rikon kwaryar ta baiwa mutanen garin Sabha da sarta wa'adin mako guda da su mika wuya ko su ma su fuskanci yaki da ake cikin yi a Libya.

Da dama daga cikin mutanen kasar ta Libya har ma da masu bin diddigin lamarin da suna yin shakku kan gaskiyar cewar an gano mabuyar Gaddafi, domin kuwa tsagerun sun sha fadin maganganu, amma daga bisani ta bayyana cewa karya ce suka shirga.

854771

captcha