Bangaren siyasa da zamantakewa; shugabannin jam'iyar Hizbul Islami a jamhuriyar Azarbaijan a karo na barkatai ta bukaci a bata izinin gudanar da taron gangami na kalubalantar daukar hana sanya hijabi a wannan kasar da kuma takurawa musulmin da ke sanye da hijabin.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; shugabannin jam'iyar Hizbul Islami a jamhuriyar Azarbaijan a karo na barkatai ta bukaci a bata izinin gudanar da taron gangami na kalubalantar daukar hana sanya hijabi a wannan kasar da kuma takurawa musulmin da ke sanye da hijabin.An nakalto daga Alcib Manaf Uf shugaban riko na wannan kungiyar a kasar ta Azarbaijan na cewa sun sake koma suna bukatar bas u dama da izinin gudanar da gagaramar zanga-zanga da taron gangami na nuna adawarsu da matakan hana sanya hijabi da takurawa masu sanye da hijabin a wannan kasa da hakan wani take hakkin dan adam ne da kuma take hakkin musulmi a wannan kasa.
886985