Bangaren siyasa da zamantakewa; musulmi a kasar Turkiya sun sake bukatar ganin an kare hakkin musulmi da hakkin mata na barin yan mata yan makaranta sanya hijabi a jami'oin kasar da cewa dole a sanya dokar kare masu hakki a cikin kundin tsarin mulkin kasar ta Turkiya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; musulmi a kasar Turkiya sun sake bukatar ganin an kare hakkin musulmi da hakkin mata na barin yan mata yan makaranta sanya hijabi a jami'oin kasar da cewa dole a sanya dokar kare masu hakki a cikin kundin tsarin mulkin kasar ta Turkiya.Wannan zanga-zanagr ta z one a daidai lokaci guda da fara taron majalisar dokoki ta kasar Turkiya da kuma za su kawo sauyi da sabbin dokoki a cikin kundin tsarin mulkin kasar kuma an samu halartar kungiyoyi masu zaman kansu masu yawa domin nuna goyan bayansu ga masu gudanar da wannan zanga-zangar.
886948