IQNA

Tsayin Dakan Iran A gaban Masu Girman Kai Shi Ne Sirrin Fadaka A kasashen Musulmi

15:51 - October 30, 2011
Lambar Labari: 2214519
Bangaren kasa da kasa, tsayin dakan da Iran ta yi a gabn siyasa zalunci da danniya ta kasashe masu girman kai shi ne babban sirrin fadakar al’ummomin musulmi da na larabawa da hakan ya kai mikewarsu da kawar da wasu daga cikin azzaluman mahukuntansu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a zantawar da ya yi da kafofin yada labarai a wurin taron baje koli na kayan sadarwa a Tehran, babban daraktan Mujallar Muslim News dag akasa Ghna ya bayyana cewa, ko shakka babu tsayin dakan da Iran ta yi a gabn siyasa zalunci da danniya ta kasashe masu girman kai shi ne babban sirrin fadakar al’ummomin musulmi da na larabawa da hakan ya kai mikewarsu da kawar da wasu daga cikin azzaluman mahukuntansu wadanda suke aiwatar da manufofin kasashen yammacin turai a cikin kasashen larabawa da na musulmi.
Abdulmannan Abdulrahman ya ce dole ne kasashen musulmi su zam acikin fadaka yadda ya kamata, domin ksashen yammacin turai wadanda su ne manyan makiya ga addinin muslumi a fadin duniya, kuma yin shiru kan abin da suke yi shi ne ya basu damar cin karensu babu babbaka kan musulmi.
Wannan tsayin dakan da Iran ta yi a gabn siyasa zalunci da danniya ta kasashe masu girman kai shi ne babban sirrin fadakar al’ummomin musulmi da na larabawa da hakan ya kai mikewarsu da kawar da wasu daga cikin azzaluman shugabanni mabiya turawa.
889163
captcha