IQNA

Za A Girmama Wadanda Suka Nuna Kwazo A gasar Hardar Kur’ani A Masar

16:49 - October 30, 2011
Lambar Labari: 2214550
Bangaren kasa da kasa, za a girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar hardar kur’ani mai tsarki da aka gudanar a kasar Masar da ta shafi wadanda suke da nakasa da ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ahram da ake bugawa akasar Masar cewa, za a girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar hardar kur’ani mai tsarki da aka gudanar a kasar Masar da ta shafi wadanda suke da nakasa da ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa kamar dai yadda aka saba kowane lokaci.
Rahoton ya ce ma’aikatar kula da harkokin addini tare da hadin gwiwa da kwamitin shiraya gasar karatu da hardar kur’ani na kasa ne za su dauki nauyi zaman taron domin giramam wadanda suka nuna kwazo adaga cikin masu shiga gasar, wanda kuma taron za a shirya shi ne a ranar bababr salla mai zuwa, tare da halartar manyan jami’an gwamnati da malaman addini
Ana shirin girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar hardar kur’ani mai tsarki da aka gudanar a kasar Masar da ta shafi wadanda suke da nakasa da ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
889119


captcha