Bangaren kasa da kasa: Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a wata ganawa da yayi da wakilan kasashe mambobi a cikin wannan kungiya da kuma wadanda ba mambobi ba a cikinsu a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa suna bin diddigin ganin Palsdinu ta zama mamba a cikin hukumar al'adu ta majalisar dinkin duniya Unesko.