IQNA

Bangaren siyasa da zamantakewa;wasu daga cikin masana da mazarta da kuma masu rajin kare hakkokin dan adam a wani zama da suka yi mai kan nazarin halin siyasa da zamantakewa a kasar aazarbaijan sun yi Allah wada da matakan takurawa da gwamnatin jamhuriyar Azarbaijan ke dauka kan masu hakokin addini a kasar inda suka bukaci gwamnatin kasar da ta rika mutunta hakkin dan adam a kasar.Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ne ya watsa rahoton cewa; wasu daga cikin masana da mazarta da kuma masu rajin kare hakkokin dan adam a wani zama da suka yi mai kan nazarin halin siyasa da zamantakewa a kasar aazarbaijan sun yi Allah wada da matakan takurawa da gwamnatin jamhuriyar Azarbaijan ke dauka kan masu hakokin addini a kasar inda suka bukaci gwamnatin kasar da ta rika mutunta hakkin dan adam a kasar. A wani taron manema labarai da suka kira bayan wannan taro da suka gudanar sun kara jaddada yin Allah wadai da matakan da mahukumta a kasar suke dauka na hana gudanar da ayyukan addini da ci gaban harkokin addini a wannan kasa a wani salo da yanayi na take hakkokin wasu daga cikin al'ummomin kasar musamman musulmi inda suka bukaci gwamnati da mahukumtan kasar da su gaggauwa kawo karshen wannan salon a take hakkin al'ummar kasar ta Azarbaijan.

897794