Bangaren siyasa da zamantakewa; bankin musulunci Imana a birnin Darul Islam fadar mulkin kasar Tanzaniya ya fara aikinsa gadan gadan.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ne ya watsa rahoton cewa; bankin musulunci Imana a birnin Darul Islam fadar mulkin kasar Tanzaniya ya fara aikinsa gadan gadan.Yan kasauwa musulmi ne dai ked a hannayen jari a cikin wannan banki bayan da suka sami izinin kafa shi daga bankin tsakiya na kasar Tanzaniya da kuma zai rika gudanar da aikinsa karkashin shari'ar muslunci har ila yau Harun Pir Muhammad shugaban komitin zartarwa na bankin Amana a wata tattauanawa day a yi da manema labarai a lokaci bukin kaddamar da bankin ya bayyana cewa; wannan bankin zai bawa kowa damar gudanar da aikinsa daidai da shari'ar musulunci.
906702