Bangaren kasa da kasa' ministocin al'adu na kasashen musulmi a mako mai kamawa ne wato a ranar ashirin da bakwai ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a Talamasan na kasar Aljeriya za su gudanar da taro domin yin dubu da bincike ci gaba da aka samu a kasashensu ta fuskar al'adu da kuma hanyoyin da za su magance matsalolin da suke fuskanta.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: ministocin al'adu na kasashen musulmi a mako mai kamawa ne wato a ranar ashirin da bakwai ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a Talamasan na kasar Aljeriya za su gudanar da taro domin yin dubu da bincike ci gaba da aka samu a kasashensu ta fuskar al'adu da kuma hanyoyin da za su magance matsalolin da suke fuskanta.Wannan shi ne taron na kasa da aksa irinsa na bakwai da ministocin da ke kula da harkokin al'adu a kasashen musulmi za su gudanar da irin wannan taro da yadda za su samu hanyoyin kara hadin kai da aiki a tare a tsakaninsu da rawar da matasa za su taka ta hanyar sulhu da tattauanawa ta fahimta na daga cikin abubuwa da za su tattauna a kai a cikin kwanaki biyu na taron nasu.
915854