IQNA

14:09 - January 01, 2012
Lambar Labari: 2249122
Bangaren siyasa da zamantakewa: ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar labanon ya jaddada cewa; duniya a yau fiye da kowa ne lokaci na bukatuwa da tunani da mahangar imam Khomeini ® da kuma na jagoran juyin juya halin musulunci na iran .Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar labanon ya jaddada cewa; duniya a yau fiye da kowa ne lokaci na bukatuwa da tunani da mahangar imam Khomeini ® da kuma na jagoran juyin juya halin musulunci na iran . Hujjatul Islam da musulmai Said Muhammad Husein Ra'is Zade mai kula da ofishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Labanon ya yi bayani kan irin koyarwa da darussan da za akoya da dogaro da su a rayuwar imam Khumeini ® wanda ya assasa jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma a rayuwar jagoran juyin juya halin musulunci kuma ga mabukata suna iya ziyartar jamhuriyar musulunci ta Iran kuma duk wanda ya yi nazari da tunani a cikin bayani da jawaban da suke gabatarwa za ga akwai koyarwa da ilmantar da mutum a matsayin san a mutum shi kadai da kuma ilmantar da jama'a da zama a bin koyi a gare su.


926212

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: