IQNA

A Jamhuriyar Tataristan An Sanyawa Wannan Shekara Ta 2012 Suna Kur'ani Mai Girma

15:56 - January 12, 2012
Lambar Labari: 2256008
Bangaren harkokin kur'ani : wannan sabuwar shekara ta miladiya ta dubu biyu da goma sha biyu a cikin wani shiri da tsari mai fadi a hauzar ilimi da yada addini a tsakanin al'ummar jamhuriyar Tataristan sun sanyawa wannan sabuwar shekara sunan shekarar Kur'ani Mai girma da fara sabuwar shekarar da koyarwa da maganar Allah mai tsarki.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; wannan sabuwar shekara ta miladiya ta dubu biyu da goma sha biyu a cikin wani shiri da tsari mai fadi a hauzar ilimi da yada addini a tsakanin al'ummar jamhuriyar Tataristan sun sanyawa wannan sabuwar shekara sunan shekarar Kur'ani Mai girma da fara sabuwar shekarar da koyarwa da maganar Allah mai tsarki. A zaman baya baya nan ne da komitin zartarwa da bin diddigin lamuran da suka shafi musulmi a kasar ta Tataristan ne suka dauki wannan mataki na sanya wa wannan sabuwar shekara sunan shekarar kur'ani mai girma. Wannan mataki da wannan komitin zartarwa ya dauka ya samu karbuwa da jinjinawa daga al'ummomin wannan kasa da kuma ganin wani mataki ne day a dace musamman ma a wannan lokaci da yanani da ake ciki ana bukatar ilmantar da jama'a alkur'ani mai girma da kuma isar da sako makamancin wannan ga sauran al'ummomin duniya musamman a kasashen musulmi.
933543

captcha