IQNA

An Fara baje Koli Ta Musamman Ta Arba'in Din Imam Huseini (AS) A Kutaif Karo Na Uku

Bangaren kasa da kasa: a karo na uku an fara gudanar da wata kasuwar baje koli ta musamman ta arba'in din Imam Huseini (AS) da aka bawa sunan Hanin Littif Jarih Shauk Ashura Khunin da aka fara a ranar ashirin da uku ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin Sanabis a lardin Kutaif da yan shi'ar Saudiya ke zaune .




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a karo na uku an fara gudanar da wata kasuwar baje koli ta musamman ta arba'in din Imam Huseini (AS) da aka bawa sunan Hanin Littif Jarih Shauk Ashura Khunin da aka fara a ranar ashirin da uku ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin Sanabis a lardin Kutaif da yan shi'ar Saudiya ke zaune .Wannan kasuwar baje kolin za a ci gaba da gudanar da ita har zuwa ranar ashirin da shidda ga watan dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da kuma a lokacin wannan kasuwar baje kolin za a nuna wa duk wannan ya ziyarci wannan kasuwar baje kolin abubuwa daban daban da suka shafi arba'in da kuma soyayyar da ke tsakanin Imam Huseini (AS) da masoya ahlul baiti (AS) .Har ila yau da abubuwa da suka shafi bayanin zalunci da rashin tausayi da aka nuna masa a yankin karbala da kuma juriya da jarumtakar day a nuna domin tsayar da addinin musulunci.
934458