IQNA

Jam’iyyar Ikhwan Ta Tsayar Da Sakatarenta A Matsayin Dan Takarar Shugabancin Majalisa

19:57 - January 18, 2012
Lambar Labari: 2259530
Bangaren kasa da kasa, jam’iyyar Ikhwan ta kasar Masar ta tsayar da sakatarenta a mtsayin dan takarar neman shugabancin majalisar dokokin kasar tsakanin ‘yan majalisar da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyarsu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, jam’iyyar Ikhwan ta kasar Masar ta tsayar da sakatarenta a mtsayin dan takarar neman shugabancin majalisar dokokin kasar tsakanin ‘yan majalisar da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyarsu da adla wal hurriyya.
Gwamnatocin kasashen lebanon da Libya sun cimma matasa dangane da makomar Imam Musa Sadr da abokan tafiyarsa biyu ta hanyar kafa wani kwamiti da zai bi kadun wannan batu da ya hada dukaknin bangarorin biyu na Lebanon da Libya.
Wani labarin da ya danganci kasar ta Lebanon da ke cewa, babban Magatarda na Majalisar Doinkin Duniya Ban Ki-moon ya soma wata ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku a kasar Labanan daga yau juma'a, domin tattauna batutuwan da suka shafi rikicin siyasar kasar Syria, da matsayin kotun da kasashen duniya suka kafa domin binciken kisan da aka yi tsohon Firayi ministan kasar ta Labanan Rafikul Hariri da kuma neman gwamnatin Labanan ta karbe illahirin makamai da kungiyar Hizbullah ta mallaka a cikin kasar.
Ban Ki-Moon zai gana da shugaban kasar ta Labanan Mishel Suleman, da Firaministan kasar Najib Mikati, da kuma shugaban Majalisar dokokin kasar Nahbih Beri wanda babban abokin kawance ne ga kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah, yayin da a gobe asabar zai gana da manyan kwadojin rundunar wanzar da tsaro.
936765

captcha