Bangaren kasa da kasa: kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar ashirin da tara ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta ke mika gaisuwar ta'aziyarta kan rasuwar Muhammad Habib Bin Khuja tsohon mai bada fatawa a kasar Tunusiya kuma shugaban hadin kungiyoyin jama'a na duniyar musulmi da kuma kusanci a tsakanin mazhabobin duniyar musulmi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar ashirin da tara ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta ke mika gaisuwar ta'aziyarta kan rasuwar Muhammad Habib Bin Khuja tsohon mai bada fatawa a kasar Tunusiya kuma shugaban hadin kungiyoyin jama'a na duniyar musulmi da kuma kusanci a tsakanin mazhabobin duniyar musulmi.Ikmalul Din Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a cikin wata sanarwa day a fitar ne ya ke bayyana bakin cikinsa da wannan babban rashi na rasuwar Muhammad Habib bin Khuja tsohon babban mai bayar da fatawa a kasar Tunusiya inda ya yi fatar alheri a gare cewa Allah sa can ta fiye masa nan kuma Allah ya karawa uyalansa hakurin wannan babban rashi mu kuma da muka yi saura Allah ya sa mu cika da imani amin summa amin.
938276