IQNA

Jakadan Haramtacciyar Kasar Isra'ila A Masar Ya Gudu Zuwa Birnin Telaviv

20:07 - January 21, 2012
Lambar Labari: 2260755
Bangaren kasa da kasa, jakadan haramtacciyar kasar Isra'ila a birin Alkahira na kasar Masar ya gudu ya koma birnin Telaviv domin tsira da rayuwarsa a lokacin da al'ummar kasar ke shirin gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na aynar gizo na tashar talabijin din Almanar ta kasar Masar cewa, Yakub Amitay jakadan haramtacciyar kasar Isra'ila a birin Alkahira na kasar Masar ya gudu ya koma birnin Telaviv domin tsira da rayuwarsa a lokacin da al'ummar kasar ke shirin gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na bababn aminin Amurka da Isra'ila a yankin gabas ta tsakiya Husni Mubarak.
Wani labarin na cewa palasdinawa biyu ne suka yi shahada a wani harin da jiragen yakin HKI suka kai a yankin Gaza a yau laraba, sannan wani guda kuma ya ji rauni.
Wani mai magana a cibiyar bada agajin gaggawa mallakar kungiyar Hamas ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa wadanda suka yi shahadar sun hada da Muhammad Abu Awda dan shekara 23 a duniya sai kuma Khalid Al-Zaanin.
Kungiyar Hamsi dai tace bata tabbatar ba ko wadanda suka yi shahadar mayakanta ne, amma wani mai magana da yawon sojojin HKI ya bayyana cewa jirgin ya kai hari ne kan wasu mayakan Palasdinawa wadanda suke kokarin dasa wasu boma bomai a kan wani shinge da suke kafa a yankin.
938370

captcha