IQNA

20:08 - January 21, 2012
Lambar Labari: 2260757
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin 'yan majlaisar dokokin kasar Kuwait da suke bin tafarkin wahabiyanci ko salafiyya suna hankoron ganin sun watsa akidar kafirta sauran musulmi akasar ta hanyar gina makarantu da suke koyar da wannan mummunar akida.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daha shafin sadarwa na yanar gizo na Iba cewa, wasu daga cikin 'yan majlaisar dokokin kasar Kuwait da suke bin tafarkin wahabiyanci ko salafiyya suna hankoron ganin sun watsa akidar kafirta sauran musulmi akasar ta hanyar gina makarantu da suke koyar da wannan mummunar akida ta wahabiyanci.
Rundunar sojin kasar Somaliya da hadin gwiwar dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika sun kaddamar da hari kan sansanonin mayakan 'yan tawayen kungiyar As-Shabab da suke birnin Mogadisho fadar mulkin kasar Somaliya a jiya juma'a.
Rahotonni sun tabbatar da cewa; Rundunar sojin hadin gwiwar sun kaddamar da harin ne da nufin kwato yankunan da suke hannun mayakan 'yan tawayen kungiyar As-Shababul- Mujahidin a cikin birnin Mogadisho, inda bangarorin biyu suka yi musayar harbe-harbe da manyan makamai, kuma rundunar hadin gwiwar sun samu nasarar kutsawa cikin yankunan da suke arewacin birnin na Mogadishu tungar 'yan tawayen na As-Shabab.
Rahotonni sun tabbatar da mutuwan fararen hula akalla 39 da sojojin gwamnatin Somaliya 4 tun bayan bullar gumurzun, sai dai har yanzu babu labarin yawan 'yan tawayen da aka kashe a dauki ba dadin.
938357
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: