Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Nun cewa, Fathi shazili tsohon jakadan kasar Masar a Saudiyya ya bayyana cewa cin zarafin mabiya tafarkin mazhabar shi’a da ake yi a kasar Saudiyya ya wuce haddi, kuma kasashen duniya suna kallo sun yi gum da bakunansu, domin kuwa gwamnatin Amurka tana goyon bayan Saudiyya kan ta’asar da take tafkawa.
Wani labarin da ya danganci kasar Lebanon da ke cewa, babban Magatarda na Majalisar Doinkin Duniya Ban Ki-moon ya soma wata ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku a kasar Labanan daga yau juma'a, domin tattauna batutuwan da suka shafi rikicin siyasar kasar Syria, da matsayin kotun da kasashen duniya suka kafa domin binciken kisan da aka yi tsohon Firayi ministan kasar ta Labanan Rafikul Hariri da kuma neman gwamnatin Labanan ta karbe illahirin makamai da kungiyar Hizbullah ta mallaka.
A tsawon wadannan kwanaki uku dai, Ban Ki-Moon zai gana da shugaban kasar ta Labanan Mishel Suleman, da Firaministan kasar Najib Mikati, da kuma shugaban Majalisar dokokin kasar Nahbih Beri wanda babban abokin kawance ne ga kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah, yayin da a gobe asabar zai gana da manyan kwadojin rundunar wanzar da tsaro ta MDD da ke kasar.
To sai dai tun kafin Ban Ki-moon ya isa a kasar, tuni kungiyar Hizbullah ta bayyana ziyarar da cewa al'ummar kasar Labanan musamman ma ma'abota 'yanci ba sa marhabin da ita.
940531