IQNA

Cibiyar Yada Al’adu da Ilimin Kasashen Musulmi Za Ta Bayar Da Babbar Kyuatarta Ta 2012

18:24 - January 28, 2012
Lambar Labari: 2263543
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar nan ta yada harkokin al’du da bunkasa ilmi a cikin kasashen musulmi ta ISESCo tana shirin bayar da babbar kyuatarta da shekara ta 2012 kamar yadda majiyar kungiyar ta sanar a cikin shafinta na yanar gizo a jiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, babbar cibiyar nan ta yada harkokin al’du da bunkasa ilmi a cikin kasashen musulmi tana shirin bayar da babbar kyuatarta da shekara ta 2012 kamar yadda majiyar kungiyar ta sanar a cikin shafinta na yanar gizo a jiya kuma da zaran ta kammala dukkanin shirye-shirye za asanar da wanda ya lashe kyautar.
Ita kuwa kungiyar Amal ta kasar Lebanon ta yi kakkausar suka tare da yin Allawadai da kisan gillar da ake yi wa masana kan harkokin nukiliya a kasar Iran tare da bayyana hakan da cewa yunkuri ne na mayar da Iran din baya a harkokinta na ilimi musamman na harkar nukiliya.
A wani labarin kuma limamin juma'a a nan birnin Tehran, ya ce kisan da makiya ke yi wa malaman kimiya na kasar, ba abin da zai cusa wa al'ummar kasar face farkawa da kuma kare martabobin kasar a kowadanne fagage na rayuwa, musamman wannan bangare na ilimimin nukiliya da Iran take ggudanar da ayyukanta a cikin na zaman lafiya domin amfanin fararen hula.
A lokacin da yake gabatar da hudubar sallar juma'a a masallacin jami'ar Tehran a yau, Ayatullahi Mohammad Emami-Kashani, ya ce kisan na baya-bayan nan da makiya suka yi wa malamin kimiyyar nukiliya na kasar mai suna Mustafa Ahmadi Roshan, wata alama ce da ke kara nuna wa duniya irin damuwar da kasashe da ke hamayya da Iran din ke da ita dangane da irin ci gaba da kuma 'yancin da kasar take da shi na dogoro da kai a fannoni na bincike da kuma kimiya.
Har ila yau limamin ya ce wasu daga cikin dalilan matsa kaimi da kasashen yamma musamman ma Amurka ke yi a kan Iran, sun hada da yadda al'ummomin kasashen wannan yanki suka juya mata baya, saboda haka suke zargin Iran da hannu a shirya irin wannan bore da ke gudana. To sai dai Ayatullah Imami-Kasheni ya ce shirun da kasashen duniya suka yi dangane da wannan ta'addanci da ake aikatawa a kan Iran, wata alama ce da ke nuna da irin goyon bayan da masu wannan shiru ke bai wa ayyukan ta'addanci a duniya.
941316

captcha