IQNA

Za A Raba Kur'anai Dubu Biyar Ga Masu Ziyara A Markadin Imam Rida (AS)

16:24 - February 02, 2012
Lambar Labari: 2267129
Bangaren adabi: babban darekta mai kula da harkokin hulda da jama'a a markadin Imam Rida (AS) ya bada labarin raba kur'anai dubu biyar ga baki wadanda ba Iraniyawa da suka ziyarci wannan guri mai albarka a cikin kwanaki goma na alfijir din nasarar juyin juya halin musulunci .

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa: babban darekta mai kula da harkokin hulda da jama'a a markadin Imam Rida (AS) ya bada labarin raba kur'anai dubu biyar ga baki wadanda ba Iraniyawa da suka ziyarci wannan guri mai albarka a cikin kwanaki goma na alfijir din nasarar juyin juya halin musulunci .Muzzafar Darabi babban darekta a ofishin da ke kula da harkokin hulda jama'a a Markadin Imam Rida (AS) ya yi bayani dalla dalla kan wannan mataki cewa wannan wani mataki ne da suka shirya a wannan shekara ta raba alkur'ani mai girma ga masu ziyara wadanda ba Iraniyawa ba a tsawon kwanaki goma na alfijir na nasarar juyin juya halin musulunci . Ya yi Karin bayanin cewa kowace rana za su raba kur'ani mai tsarki dari biyar .
945143
captcha