Bangaren harkokin kur'ani mai girma: cibiyar kula da al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a birnin Delhu No na kasar Indiya a daidai lokaci guda na fara makon hadin kai a tsakanin musulmi ta shirya gasar karatun kur'ani mai girma da harda a fadin kasar ta Indiya daga ranekun sha bakai zuwa sha tara ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya karkashin sa idon wakilin hukumar kula da al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a wannan kasa.