IQNA

Za A Bude Wata Kungiya Ta Duniya Ta Yin Nazari A Cikin Kur'ani A Katar

14:29 - February 08, 2012
Lambar Labari: 2271347
Bangaren kasa da kasa: a yau ne sha tara ga watan bahmain na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya karkashin himmar ma'aikatar da ke kula da harkokin addinin musulunci a kasar Katar za ta bude wata kungiya ta duniya da za ta rika gudanar da nazari da bincike a cikin kur'ani mai girma.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Irn ne ya watsa rahoton cewa; a yau ne sha tara ga watan bahmain na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya karkashin himmar ma'aikatar da ke kula da harkokin addinin musulunci a kasar Katar za ta bude wata kungiya ta duniya da za ta rika gudanar da nazari da bincike a cikin kur'ani mai girma.A daren yau ne za bude cibiyar wannan kungiya ta duniya da za ta rika gudanar da aikin bincike da nazari a cikin ayoyin kur'ani mai girma kuma za a samu halartar Gait Bin Mubarak Alkawari ministan da ke kula da harkokin addini a kasar ta katar da kuma wasu daga cikin fitattun malamai da masana kur'ani a ciki da wajan kasar ta Katar. Wannan kungiya za ta rika gudanar da aikinta day a shafi rubuce rubuce da raya sunnar yin nazari da tunani a cikin ayoyin kur'ani mai girma ,wannan na daga cikin muhimman ayyukan da wannan kungiya za ta gudanar .
949053
captcha