IQNA

Bangaren hauzar ilimi:Sheikh Tajjul Dine Hilali a daidai lokacin da yake bayani kan hadisin Sakalain da suka zo a cikin manyan littafan Ahlul Sunna ya jaddada cewa:al'ummar musulmi ya kamata su nemi afuwa ga ma'aikin Allah mai girma tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka saboda yadda aka canja wasiyarsa da hakan ke a matsayin cin amanarsa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Sheikh Tajjul Dine Hilali a daidai lokacin da yake bayani kan hadisin Sakalain da suka zo a cikin manyan littafan Ahlul Sunna ya jaddada cewa:al'ummar musulmi ya kamata su nemi afuwa ga ma'aikin Allah mai girma tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka saboda yadda aka canja wasiyarsa da hakan ke a matsayin cin amanarsa.A ranekun sha bakwai das ha takwas ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka gudanar da taron hadin kai a tsakanin musulmin duniya da aka samu halartar shugabannin Hauzar Ilimi ta Tehran da malaman Hauza na birnin a kamarantar ilimi ta imam Khomeini da ofishin da ke kula da harkokin kasa da kasa da shugabannin Hauza ya shirya.Kuma malamai da jagororin addini da dama ne suka gabatar da jawabi a gurin wannan taro da a cikin jawaban suke jan hankalin musulmin duniya das u hada kansu musamman a daidai wannan lokaci da makircin makiya ke kara yawaita da muni kan kasashen musulmi da muslmi .

950028