Bangaren fikira, wadanda suke kallon duk abin da yake wajen dabia ta rayuwa da aka saba ita, da kuma abubuwa da ake gani na duniya wadanda ake iya taba su ko ganinsu da jinsu a jika, wannan bangare ne na irfani na karya da baya da tushe a mahangar addini.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Hojjatul Islam Dr. Mu’ahhad Taqi Fali ya sheda cewa malamin jami’a kuma malamin Hauza ya ce wadanda suke kallon duk abin da yake wajen dabia ta rayuwa da aka saba ita, da kuma abubuwa da ake gani na duniya wadanda ake iya taba su ko ganinsu da jinsu a jika, wannan bangare ne na irfani na karya da baya da tushe a mahangar addini, domin kuwa addini ya yi amanna da gaibi da kuma abubuwan wajen dabi’a.
Zai yi kyau mu kammala kalaman mu na ziyarar kabrukan A’imma (as) tare da yin ishara ga wasu muhimman abubuwa guda biyu da suka zo a cikin labarai, sai dai za mu iya ishara zuwa gare su a takaice, amma ga maso son karin bayani sai su duba littatattafan dake bayani kan akida da suka shafi wannan bayani.
Abin la'akari na farko: wajibi ne ga mai ziyarar kabarin A’imma ya nisanci aikata duk wani aiki da zai nuna alamun shirka ga Allah a cikinsa, kamar nuna bauta ga ma'abocin kabarin, shi yasa ma kamar yadda ya zo a cikin hadisai da aka rawaito daga gare su da madogara karbabbiya daga Imam Bakir (as) za ka ga cewar iyalan gidan manzo suna hani ga aikata irin wadan nan ayyuka. An rawaito daga Zurara daga Abi Ja'afar (as) wani mutum ya ce masa: yaya batun yin sallah tsakanin kabari? Sai ya ce: a'a ka yi sallah a gefensa kada ka riki wani abu daga gare shi a matsayin alkibla domin manzo (saww) ya hana yin haka, kuma ya ce kada ku riki kabarina al kibla ko kuma masallaci, domin Allah madaukakin sarki ya la'anci wanda suka riki kabrurrukan Annabawansu massallaci.
Haka nan kamar yadda ya zo a wata ruwaya ta daban da aka amince da ita inda akayi hani na (shiryaswa ba wai na haramci ba). Game da yin dawafi a kabari , An rawaito daga halabi daga Abi Abdallah (as) ya ce, karkasha wani abu kana tsaye, kada ka yi dawafi a kabari.
Babu shakka abin da ake nufi da hani a nan na kada a rike kabari a matsayin alkibla ko kuma masallaci da kuma dawafi a kansa, shi ne mutum ya maida kabarin da kansa alkibla ko kuma massalaci, bai halarta a yi sujuda a kansa ba ko kuma a fuskance shi a cikin sallah, ba wai kawai ya kasance a wurin da massallata suke fuskanta ba ko kuma kafa massalatai ko yin gine gine a kabarin. Shi dai wannan hani kamar yadda ya zo, ana iya fahimtar cewar kamar misalin hukunci ne da maudu'insa kawai, ana nufin hani domin tsarkake shi daga duk wata bauta ne.
Yana daga cikin abubuwan da suke karfafa wannan waiwaye da muka yi na batun jaddadawa kan tauhidi, wato kadaita ubangiji da aka fadi a cikin wasu ziyarori da muka kawo da suka hada da batun kabbara, da kuma godiya ga Allah a kan samun dacewar da aka yi, da kuma gode masa a kan ni'imar da ya yi mana da kuma kusanci ga manzo da iyalan gidansa tsarkaka, domin sun tsaida sallah, sun bada zakka, sun yi umarni da kyakayawan aiki sun yi hani ga mummunan aiki, kuma sun yi jihadi saboda Allah bisa gaskiya, sun isar da sakon Allah da dai sauran kalamai makamantan haka da suke da alaka kai tsaye da tauhidin ubangiji.
Abu na biyu: da ya kamata a yi la'akari da shi, yana da kyau a yi la'akari da cewar ziyarar manzon Allah da iyalan gidansa da aka kawo a irin wadannan wurare da kuma inda aka bizne su, ana yinsu ne kawai a mtsayin neman tabarruki tun da su rayayyu ne a wurin ubangijinsu ana azurta su, kamar yadda Allah yake cewa a cikin al kur’ani, domin suna jin maganganun mu suna maida mana da sallama, da kuma ba mu amsa a kan tambayayoyinmu, don haka ne ma ake son mutum da zai kai musu ziyara ya kasance ya fahimci dukkan ma'noni da suke kunshe a cikin ziyarorinsu (as) da zai tabbata gare shi kamar lokacin da suke raye na abin da ya shafi wulayarsu ne, da kuma bayyana abin da zai nuna kaunarsu da kyautatawa, saboda kusantar su da aka yi da kuma girmamawa da yi musu biyayya da kuma koyi da su, bawai ziyara tasu ta kasance domin neman abin duniya ba ne kawai, dake nuna tamkar girmamawa ga mamatan da kasusuwansu, da dai sauran wasu ma’anoni da suke da alaka da abin da ya shafi neman duniya kai tsaye, da babu wani imani da Allah a cikinsa ko kuma rayuwar ta har abada, wato lahira ga wadanan rayuka masu tsarki, wanda hakikain ziyara ana yin ta ne ga shi zatin da ke wanzuwa ya ci gaba da rayuwa daga abin da ubanjigi ya kebance shi da shi, da kuma irin alakar da yake da shi tsakninsa da mahalicci, da kuma irin karba kiran ubangiji game da umarnin da ya bayar na yi musu da'a da taimakonsu da kuma girmama su.
Hakika An rawaito a cikin wasu ruwayoyi da suka fito daga madogarai masu karfi daga Imam Ja'afar Sadiq (as) cewa ya ce: babu wani Annabi ko kuma wasiyin Annabi da zai kasance a bayan kasa fiye da kwanaki uku, face Allah madaukakin sarki ya daukaka ruhinsa da kasusuwansa da naman jikinsa zuwa sama, amma ana zuwa ziyarar su a kufansu ne domin suna amsa sallama daga nesa kuma ana jinsu a wuraren kufansu daga kusa.
925995