Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarkin a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; cibiyar da ke kula da addinin musulunci a Britaniya ta kaddamar da wata bazarar karatu da koyar da karatun kur'ani mai girma da hukumce-hukumce na musulunci ga wadanda bas u jima da karbar addinin musulunci a birnin London fadar mulkin kasar.Wannan bazarar karatun da bada horan ga sabbin shiga addinin musulunci a kasar ta Britaniya za a ci gaba da bayar das hi har zuwa ranar biyar ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya mai kamawa. Kuma an kasa su kaso uku ajin farko da na tsakatsakiya da kuma na wadanda suka ci gaba kuma ana koya masu dokokin tajwidi na karatun kur'ani mai girma kuma tuni musulmi daga cikinsu suka nuna gamsuwa da farin cikinsu kan wannan mataki tare da jinjinawa shugabannin wannan cibiya .
955156