IQNA

An Tabbatar Da Wajabcin Karfafa Demokradiyya A Harkokin Mulki A Bahrain

22:33 - February 20, 2012
Lambar Labari: 2277790
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zamna taro a kasar Bahrain da nufin nuna cikakken goyon baya ga al’ummar kasar da suke boren neman ‘yanci inda aka jaddada wajabcin kafa gwamnati mai bin sahihin tafarki na demokradiyya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na mepanaroma cewa, an gudanar da wani zamna taro a kasar Bahrain da nufin nuna cikakken goyon baya ga al’ummar kasar da suke boren neman ‘yanci inda aka jaddada wajabcin kafa gwamnati mai bin sahihin tafarki na demokradiyya da baiwa kowa ‘yancinsa na siyasa da biya ma mutane hakkokinsu da aka haramta musu.
Tsohon shuagaban kungiyar leken asrin haramtacciyar kasar Isara'ila Mossad Auzy Dayan ya bayyana abin da ke faruwa a kasar Syria cewa zai amfanar da Isra'ila ta fuskoki da dama.
Dayan ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da gidan radiyon Tel aviv, inda ya sheda cewa ci gaba da riki a kasar Syria zai raunana kawancen da ke akwai tsakanin Iran da Syria da kuma kungiyar Hizbullah, domin kuwa wannan kawancen shi ne babbar barazana ga yahudawan sahyuniya, ya ce za su ci gaba da taimaka ma 'yan adawae kasar Syria domin kawo karshen mulkin Bashar Asad.
A nasa bangaren ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra'ila Avigdor Lieberman ya tabbatar da cewa suna da kyakyawar dangantaka da 'yan adawar Syria, kuma suna ba su dukaknin taimako da nufin kawar shugaba Asad daga shugabancin Syria.
956047

captcha