IQNA

Iran Ce Kawai A Halin Yanzu Ta Zama Abin Da Musulmi Suke sa Rai A kanta

22:32 - February 20, 2012
Lambar Labari: 2277794
Bangaren zamantakewa, a halin yanzu jamhuriyar muslunci ce kawai kasar da musulmin duniya suke sa ran za ta iya tabuka wani abun azo a gani domin kare musulmi da musulunci a matsayi na duniya daga sharrin makiya domin kuwa akasarin kasashen musulmi da na larabawa sun zama ‘yan amshin shatar Amurka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a lokacin da yake gabatar da wata lacca kan makomar kasashen musulmi a birnin Berlin na kasar Jamus kamal Halbawi ya sheda cewa, a halin yanzu jamhuriyar muslunci ce kawai kasar da musulmin duniya suke sa ran za ta iya tabuka wani abun azo a gani domin kare musulmi da musulunci a matsayi na duniya daga sharrin makiya domin kuwa akasarin kasashen musulmi da na larabawa sun zama ‘yan amshin shatan kasashen yammacin turai da yahudawa.
Cikin 'yan kwanakin nan dai kasashen Saudiyya da Qatar bisa goyon bayan Amurka da HKI sun matsa kaimi cikin kulle-kullen da suke yi kan kasar Siriya da nufin dagula lamurra a wannan yanki na gabas ta tsakiya don cimma manufofin kasashen yammaci da tabbatar da tsaro ga HKI.
Sakamakon farkawa ta Musulunci da ta kunno kai a kasashen musulmi da na larabawa da ta yi sanadiyyar kifar wasu shugabanni 'yan kama-karya, a bangare guda kuma ta kara sanya muggan manufofin Amurka a wannan yankin cikin hatsari ga kuma irin saniyar waren da HKI take ci gaba zama a irin wadannan kasashen, hakan ya sanya Amurka, HKI da kuma kawayensu daga cikin kasashen larabawa shigowa fage da kuma yin dukkanin abin da za su iya wajen ganin sun kawar da irin wannan farkawa ko kuma alal akalla raunanata, a bangare guda kuma da yin dukkanin abin da za su iya wajen ganin sun kawo karshen akidar gwagwarmaya da neman 'yanci a wannan yankin wanda ke barazana ga muggan manufofinsu. Daya daga cikin hanyoyin cimma hakan kuwa ita ce kawar da gwamnatoci masu goyon bayan gwagwarmaya da kuma tsayin daka na al'ummomi irin su gwamnatin kasar Siriya.
Don cimma wannan manufar kuwa, Amurka da sauran kasashen yammaci sun bukaci kasashen Saudiyya da Qatar da su wuce gaba da daukan matakan da suka ga ya dace ciki kuwa har da ba wa kungiyoyin 'yan ta'adda masu adawa da gwamnatin Bashar Al-Asad ta Siriyan makamai duk dai da nufin kifar da gwamnati don su sami damar kafa wata gwamnati wacce za ta biya musu bukatunsu. Wata hanyar kuma ta daban ita ce kokarin mai da lamarin kasar Siriya ya zamanto wani lamari na kasa da kasa da shigo da manyan kasashen duniya cikin lamarin.
956020
captcha