Bangaren kasa da kasa: hukumar da ke kula da harkokin al'adu na musulunci na Asesko a ranar hudu ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da babbar murya kan yadda wasu sojojin Amerika yan mamaye a kasar Afganistan suka cinnawa kur'anai masu daraja wuta.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: hukumar da ke kula da harkokin al'adu na musulunci na Asesko a ranar hudu ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da babbar murya kan yadda wasu sojojin Amerika yan mamaye a kasar Afganistan suka cinnawa kur'anai masu daraja wuta. Hukumar t ace kona kalaman Allah madaukakin sarki wato cinnawa kur'ani mai girma wuta wani babban lamari ne day a shafi nunwa wariya da banbancin addini da kuma mataki na takalar fada kuma musulmin duniya ba za su taba manta wannan danyan aiki da kuma matakin tada fitina da nuna karan tsana da wariya kan addinin musulunci. Hukumar ta bukaci a gurfanar da wadanda suka aikata wannan aiki a gaban komitin kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya kuma da kalubalantar matakan da sojojin kungiyar tsaro ta Nato karkashin jagorancin Amerika ke dauka.
959226