Bangaren al'adu da fasaha: littafin risalatun Hukuk ta imam Zainul Abidina (AS) an fassara ta a cikin yaren kasar Bulgairiya da kuma yada ta a fadin kasar kuma ai dauki dawainiya fassara wannan littafi mai muhimmanci tsakanin hukumar da ke kula da mabiya Ahlul baiti (AS) ta duniya da kuma ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a wannan kasa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; littafin risalatun Hukuk ta imam Zainul Abidina (AS) an fassara ta a cikin yaren kasar Bulgairiya da kuma yada ta a fadin kasar kuma ai dauki dawainiya fassara wannan littafi mai muhimmanci tsakanin hukumar da ke kula da mabiya Ahlul baiti (AS) ta duniya da kuma ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a wannan kasa. Wannan littafi na risalatul Hukuk na imam Zainul Abidine (AS) ta kumshi hakkoki daban daban kama da hakin dake tsakanin mutum da mahaliccinsa da kuma sauran hakkoki da ke tsakanin mutane a daidaiku da a jama'ance kamar hakkin uwa kan dansa ko hakkin uwa kan danta da kuma hakkin dad a ked a shi kan uwayansa ko hakkokin da ke tsakanin mata da miji da sauran hakkoki iri daban daban kuma a fayyace karara.
963046