IQNA

Musulmi Ba Za Su Jurewa Cin Mutuncin Kur'ani Daga Masu Raya Kare hakkin Dan Adam

12:35 - March 01, 2012
Lambar Labari: 2283617
Bangaren siyasa: shugaban alkalai a kotun koli ta jamhuriyar musulunci ta Iran ya yi nuni da cewa cin mutuncin kur'ani mai girma da sojojin mamaye na Amerika suka yi a Afganistan da cewa; musulmin duniya ba za su yi shiru da kale wannan cin fuska ga wadanda ke raya kare hakkin dan adam a duniya.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; shugaban alkalai a kotun koli ta jamhuriyar musulunci ta Iran ya yi nuni da cewa cin mutuncin kur'ani mai girma da sojojin mamaye na Amerika suka yi a Afganistan da cewa; musulmin duniya ba za su yi shiru da kale wannan cin fuska ga wadanda ke raya kare hakkin dan adam a duniya.Ayatullahi Sadik Amuli Larjani shugaba alkalin alkalai na jamhuriyar musulunci ta Iran a yau goma ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani zam na alkalai na kasar bayan ya taya murna da zagayowar irin wannan rana ta haifuwar Imam Hasan Askari (AS) yayi Allah wadai da yadda siyasar takalar fada da tsangwama ta gwamnatoci da shugabannin yammacin turai ke ci gaba da yin Allah wadai da yadda a yan kwanakin nan wasu sojojin mamaye na Amerika a kasar afganistan suka kona wasu kur'ani da cewa har abada musulmi a fadin duniya ba za su yafe bad a kuma manta wannan lamarin na cin fuska da cin mutuncin addini da littafinsu mai daraja da daukaka.


963146
captcha