Bangaren fikira da ilimi, an gudanar da wani zaman tattaunawa dangane da matsayin mata da kuma irin rawar da suke takawa a cikin harkokin rayuwar jama'a na zamantakewa, wanda cibiyar ilimi ta hauza ta dauki nauyin gudanarwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da wani zaman tattaunawa dangane da matsayin mata da kuma irin rawar da suke takawa a cikin harkokin rayuwar jama'a na zamantakewa, wanda cibiyar ilimi ta hauza ta dauki nauyin gudanarwa a cikin wannan mako da muke ciki.
Hujjatul islam Alibuwaihiya bayyana a wajen wannan taron cewa, wasu daga masana da kuma marubuta a cikin wanna karni sun mayar da hankali kan batutuwa da suka danganci matsayin mata da kuma irin rawar da za su iya takawa, amma abun ban takaicin shi ne yadda suka kasa fahimtar cewa mace tana da matsayi na musamman, wanda ba dole ne sai ta yi dukaknin abin da namiji zai bi ba ne ta zama mutum.
A karshen zaman da dama daga cikin masu nazari da kuma mambobin tawagar bunkasa harkokin ilimi da bincike kan harkokin mata, sun gabatar da nasu mahanr kan yadda mata za su karfafa jikinsu ta hanyoyi da dama.
964397