IQNA

Cibiyar Yada Al'adun Musulunci ta Yi Allawadai Da Keta Alfarmar Kur'ani

20:55 - March 06, 2012
Lambar Labari: 2286941
Bangaren kur'ani, cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun musulunci ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamamyar Amurka suka yi a kasar Afghanistan tare da bayyana hakan da cewa wani mataki na tsokanar dukaknin musulmi na duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun musulunci ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamamyar Amurka suka yi a kasar Afghanistan tare da bayyana hakan da cewa wani mataki na tsokanar dukaknin musulmi na duniya ta wannan hanya, ta yadda hakan zai zama wani masomin rikici.
Bayanin da cibiyar ta fitar y ace dole ne usulmi su zama cikin fadaka kan makircin da ake kitsa musu, kuma yin hakan zai ba su damar tabbatgar da izzar addininsu, da kuma kar ababe masu tsarki da ke cikin addininsu, domin kuwa keta alfarmar kur'ani, keta alfarmar dukaknin musulmin duniya ce, wanda hakan ya ratay kan musulmin ne.
Wannan cibiyar ta bunkasa harkokin ilimi da al'adun musulunci ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamamyar Amurka suka yi a kasar Afghanistan tare da bayyana hakan da cewa wani mataki na tsokana. 965561
captcha