IQNA

Da Gangan Ne Sojojin Amerika Suka Kona Ku'ani Mai Girma

14:16 - March 07, 2012
Lambar Labari: 2287474
Bangaren siyasa da zamantakewa; sabanin abin da mahukumtan Amerika ke yadawa ,komitin bincike a jamhuriyar musulunci ta Afganistan ya bada labarin cewa: da gangan ne wasu sojojin mamaye na Amerika a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan suka suka dauki matakin ganganci na kona kur'ani a wani matakin cin mutunci ga littafin mai daraja da daukaka na musulmi.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: sabanin abin da mahukumtan Amerika ke yadawa ,komitin bincike a jamhuriyar musulunci ta Afganistan ya bada labarin cewa: da gangan ne wasu sojojin mamaye na Amerika a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan suka suka dauki matakin ganganci na kona kur'ani a wani matakin cin mutunci ga littafin mai daraja da daukaka na musulmi.Sakamakon binciken da komitin bincike a kasar Afganistan ya gudanar kan wannan mummunan aiki da takalar fada da wasu sojojin mamaye na Amerika a Afganistan suka yin a nuni da cewa da aikin ganganci ne wadannan sojoji na Amerika suka yin a kona kur'anai a kasar ta Afganistan kuma abin da suka aikata ya sabawa abin da mahukuntan Amerika suke bayyanawa musmman komandan sojojin Amerikan a Afganistan . Khalik Dad mamba a komitin y ace wannan abu ba za a taba yafewa ba domin bincike ya nuna aikin ganganci ne kuma da sani aka aikata hakan.
966700

captcha