A cewar gidan talabijin na Aljazeera, Valentina Gomez, 'yar takarar jam'iyyar Republican a zaben majalisar dokokin Amurka daga Texas, ta saka wani faifan bidiyo mai kyama a kafar sadarwar X inda ta kona kur'ani.
Yayin da take wulakanta kur'ani mai tsarki, ta yi alkawarin kawo karshen kasancewar addinin Musulunci a jihar Texas idan ta lashe zaben 'yan majalisar dokokin Amurka.
Wannan mai kyamar Musulunci, da kuma ke da tarihin goyon bayan shugaban Amurka Donald Trump, ta yi ikirarin cewa musulmi na neman mamaye kasashen Kirista.
'Yar takarar majalisar dokokin Amurka ta bukaci masu kallon wannan faifan bidiyo na nuna kyama da su taimaka mata ta lashe zaben majalisar.
Matakin na yar siyasar na Amurka mai tsattsauran ra'ayi ya jawo kakkausar suka daga shugabannin siyasa, kungiyoyin addinai da masu amfani da shafukan sada zumunta, lamarin da ya kara nuna damuwa game da yaduwar kalaman kyama da kyamar addini gabanin zaben tsakiyar wa'adi na 2026.
Gomez ta yi amfani da kalaman kiyayya don samun suna a baya. A cikin Disamba 2024, ta yi kira da a aiwatar da hukuncin kisa a bainar jama'a kan baƙi da ake zargi da aikata laifukan tashin hankali. Daga baya an cire bidiyon kuma an dakatar da asusun Gomez na Instagram.
Duk da wadannan abubuwan da suka janyo cece-kuce, Gomez ta sha kaye a zaben da ya gabata, inda ta samu kashi 7.4% na kuri'un da aka kada a zaben cikin gida na jam'iyyar Republican, ta kuma zo na shida.