IQNA

Kiristan Nan Mai Cin Zarafin Kur'ani Ya Goyi Bayan Wadanda Suka Kona Kur'ani A Afganistan

12:54 - March 17, 2012
Lambar Labari: 2292935
Bangaren kasa da kasa;Tery Jonz kirsitan nan mai tsautsoran ra'ayi dan kasar Amerika wanda ya shahara wajan cin zarafin kur'ani mai tsarki a wani shafin Internet ya aike da wani sakon goyan baya ga sojojin da suka kona kur'ani a Afganistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: Tery Jonz kirsitan nan mai tsautsoran ra'ayi dan kasar Amerika wanda ya shahara wajan cin zarafin kur'ani mai tsarki a wani shafin Internet ya aike da wani sakon goyan baya ga sojojin da suka kona kur'ani a Afganistan. An jiyo daga majiyar labarai ta Al-kanz cewa Teru Jonz shugaban cocin mutane hamsin ta Dav Bvbard Taric a lardin Florida na Amerika da a shekara ta dubu biyu da goma yayi barazanar kona kur'ani mai tsarki a wani sabon karo ya sake fitowa yana tankalar fada kan musulmin duniya inda ya nuna goyan bayansa dari bias dari ga sojojin Amerika da ke gudanar da aikin mamaye a kasar Afganista karkashin kungiyar tsaro ta Nato da cewa: yana da niyar kirkiro da wani dandani na duniya na kona kur'ani mai tsarki a gurin musulmi.Wannankiristan mai neman tada fitin ada rikici a tsakanin musulmi da kirista ya raya cewa yayi wannan bayani ne domin kare kirsitoci da hakkokinsu a yankin gabas ta tsakiya dab a a karewa da nuna masu banbanci sai dai tuni kirsitoci suka yi watsi da wannan abu da yake rayawa da ganinsa a matsayin mai neman haddasa rikici da fitina a tsakanin musulmi da kiristoci a fadin duniya da fatar Allah ya maida masa mummunar aniyarsa.

972905

captcha