IQNA

An Bude Darul Kur'ani Ga Mata A Jodan

16:40 - March 26, 2012
Lambar Labari: 2294872
Bangaren kasa da kasa: a garin Sultan na kasar Jodan ne ak bude darul kur'ani na musamman ga mata kuma lokacin bude wannan cibiya ta kur'ani an samu halartar Aud Alfa'uri shugaban ofishin kula da harkokin addini a garin.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya tsawa rahoton cewa: a garin Sultan na kasar Jodan ne ak bude darul kur'ani na musamman ga mata kuma lokacin bude wannan cibiya ta kur'ani an samu halartar Aud Alfa'uri shugaban ofishin kula da harkokin addini a garin.Jaridar aldastur da ake bugawa a kasar jodan ne ta bada labarin cewa: AlFa'uri a wajan wannan buki na kaddamar da darul Kur'ani ya gabatar da jawabi da cewa; kaddamar da bude irin wannan cibiya ko darul ky=ur'ani na koyar da karatun mai girma wajibi ne kuma laruri. Ya kara da cewa: wannan shi ne darur kur'ani irinsa na biyu da aka kafa a wannan gari yayin da na farko ya shafi koyar da maza karatun kur'ani mai girma sai kuma gashi yanzu an bude wani darur kur'ani na musamman ga mata zalla da hakan ke nuni da yadda mutanan garin ke bawa karatun kur'ani muhimmanci da daraja ta musamman a kuma fatar ganin sauran al'ummo a garuruwa daban daban na kasar sun yi koyi da al'ummar garin Sulta.

974735
captcha