IQNA

Gasar Karatu Da Hardar Kur'ani Mai Girma Ga Yaran Tatar

15:40 - March 28, 2012
Lambar Labari: 2295496
Bangaren harkokin kur'ani mai girma: an shirya wata gasar karatun kur'ani mai girma da kuma hardarsa da aka yi a ranar shida ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da aka shiryawa yara kanana na Tatar a babban masallacin garin Najani Kamsak na jamhuriyar Tataristan.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an shirya wata gasar karatun kur'ani mai girma da kuma hardarsa da aka yi a ranar shida ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da aka shiryawa yara kanana na Tatar a babban masallacin garin Najani Kamsak na jamhuriyar Tataristan. Wannan gasar tana daga cikin shirin da aka tsara za a gudanar a cikin wannan shekara ta dubu biyu da goma sha biyu miladiya na shiryawa yara karatun kur'ani mai girma da kuma hardasa tare da faraway da yara maza arba'in da suka fito daga yankuna daban daban na kasar da kuma takwarorinsu yan mata talatin .An shirya masu gasar ne a cikin juzi'I sha biyar da kuma goma da kuma duk inda yaro ke son yin gasa a kansa kuma an samu halartar malamai dam asana da kuma musulmi da suka halarci gurin wannan gasar kuma aka bayar da kyauta mai kima ga wadanda suka ci nasara wannan gasar.

975672
captcha