Bangaren kasa da kasa: a ranar sha uku ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne a birnin Maskat fadar mulkin wannan kasa aka fara gudanar da matakin karshe na gasar karatun kur'ani mai girma a wannan kasa ta Oman kuma wannan gasar karatun kur'ani mai girma ta hada har da hardar Kur'anin.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a ranar sha uku ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne a birnin Maskat fadar mulkin wannan kasa aka fara gudanar da matakin karshe na gasar karatun kur'ani mai girma a wannan kasa ta Oman kuma wannan gasar karatun kur'ani mai girma ta hada har da hardar Kur'anin.Majiyar Labarai ta ONA News ta bayyana cewa makaranta kur'ani Mai girma dari biyu da tamanin da biyar ne day a hada makaranta da mahardata kur'ani suka fafata da juna har zuwa ranar ashirin da bakwai ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da ta gabata amma wannan karo makaranta da mahardata Kur'ani Mai Girma dari da arba'in da biyu ne za su fafata da juna a matakin karshe na wannan gasar kur'ani mia girma a fannoni daban daban da suka hada hard a tajwidi.
977144