Bangaren siyasa da zamantakewa; a ranar biyu ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a babban dakin taro na jami'ar musulunci da ke kasar Rasha aka fara gudanar da wani taron karawa juna sani kan tattalin arziki irin na musulunci da bangaren da ke kula da harkokin da suka shafi kasuwanci das aye da sayarwa irin na musulunci da zamanatakewa ya shirya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a ranar biyu ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a babban dakin taro na jami'ar musulunci da ke kasar Rasha aka fara gudanar da wani taron karawa juna sani kan tattalin arziki irin na musulunci da bangaren da ke kula da harkokin da suka shafi kasuwanci das aye da sayarwa irin na musulunci da zamanatakewa ya shirya. A wajan wannan taron an samu halartar masana da kwararru a harkar tattalin arziki das aye da sayarwa kuma yan jami'a da malaman jami'a da dama ne suka halarci wannan taron na karawa juna sani tare da takwarorinsu malaman addini da musulmi a wannan kasa ta Tataristan .kuam da dama daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a gurin wannan taron sun yi bayani mai gamsarwa da kuma jan hankali kan muhimmancin bin tsari irin na addinin musulunci a fuskar tattalin arziki musamman a daidai wannan lokaci da ake fuskantar matsalar tattalin arziki a manyan kasashe na yammacin turai.
991213